#SIHIRIN #SOYAYYA #SIHIRINCUTA
Ga wata Tambaya:
Wani lokaci a wasu nau'in sihrai kamar sihirin soyayya, ana yin sihirin tare da cutar da wanda aka yi masa sihirin a lokaci guda?
Shin akwai haÉ—in kai tsakanin sihirin soyayya da sihirin cuta wanda yake haddasa rashin lafiya wani lokaci?
Shin wannan ya shafi sauran nauikan sihrai kuma?
Amsa: Ban san akwai haÉ—in kai tsakanin sihirin soyayya da sihirin cuta ba, wanda yake haddasa rashin lafiya.
sai dai idan sihirin ya fita daga hanya da ya kamata ya bi.
Amma sihirin raba aure zai iya É—aukar nau’in sihirin cuta, mai haddasa rashin lafiya da nufin idan mutum ya yi rashin lafiya ya yi zafi da yawa, sai sauran mutumin ya Æ™i shi ya gajiya da zamansa da shi ya rabu dashi daganan.
Wallahu aalam.
Tambaya. Wasu ruwayoyi suna cewa zafin Æ™asan baya alama ce tabbatacciya ta sihiri. Menene ra’ayinka, Malam?
Amsa:Idan haka ne to kusan kashi uku cikin huÉ—u na duniya an yi musu sihiri.
Tambaya: Ruwayar yana nufin zafin baya na cutar ruhaniya, ba na jiki ba. Yana cewa alama ce ta sihiri?
Amsa: Yawanci haka yake, amma ba a kowane hali ba. Hassada da cutuka ido ma na iya haddasa haka, Allah ne mafi sani.
Wannan yanki yana da alaka da jin mutum na kwanciyar hankali, tsaro, kwanciyar hankali da haÉ—in kan iyali. Baya ga haka kuma yana aiki a matsayin cibiyar sha’awar jima’i.
Tambaya: To, shin idan zafin ƙasan baya ya samo asali ne daga hassada, zai sa mutum ya ji rashin tsaro da rashin kwanciyar hankali a gida?
Amsa:I, har ma wasu matsalolin hankali ma kan sa haka wani lokaci.
Tambaya:Wasu masu sihiri hannayensu kan yi motsi kamar na wasan kwaikwayo, su koma baya lokacin ruqiya. Suma daga gida É—aya ne. Menene wannan motsin yake nufi, Malam?
Amsa:Motsin kwaikwayo yana da dalilai da yawa. A da muna tunanin duka saboda sihiri ne.
Amma da muka bincika sai muka ga wanda aljanin ƙarin ya shige shi, ko wanda kuzarin da ba shi da kyau ya yi yawa a jikinsa, hakan yana faruwa.
Kuma yana yiwuwa a cikin haka akwai sihiri.
Allah ne mafi sani.
#Muhd #Jameel #Jaafar
Aljerian Islamic Chemist

No comments:
Post a Comment