Na'a-na'a [Peppermint/mentha piperita or mint]
wata shuka ce mai albarka da ake amfani da ita a
matsayin maganin gargajiya. Ganyen na'a-na'a
kore ne, kamshin ta nada karfi, tana da kamshi
mai dadin gaske da filebo mai sanyaya rai. Na'a-
na'a nada sinadarin 'minti' ( wato 'menthol') mai
sanyaya rai da lafiyar jikin dan adam. Akanyi
amfani da na'a na'a wajen sarrafa wasu kayan
amfanin gida da muke siya na yau da kullum,
wato kayan amfani da muke siya a kasuwa kamar
irinsu makilin (toothpaste), sabullai (soaps), man-
shafawa (creams and vaselines), cingam (chewing
gum), sinadarin wanke baki (mouthwash) ,
magungunan shafawa (ointments), da sauransu ,
saboda kamshinta da amfaninta ga jikin dan
adam.
Bincike ya nuna cewa, shukar na'a-na'a dai ta
samune asali ta hanyar auren-shuka , wato auren
shuka mai suna 'watermint' da turanci da kuma
wata shukar mai suna 'spearmint'. Bincike ya nuna
cewa na'a na'a tazo ne daga kasashen turawa da
larabawa. Mutanen wadannan kasashen da muka
ambata kanyi amfani da ganyen na'a-na'a cikin
abinci da kuma wajen shayi, a matsayin ganyen-
shayi (tea leaves) haka kuma, akwai man -na'a
na'a ( peppermint oil) da ruwanta (peppermint
water) a kasuwa domin amfani na daban-daban.
Bincike ya nuna cewa na'a-na'a nada amfani da
yawa ga lafiyar dan adam. Wasu daga cikin
amfaninta ga jikin mutum sune:
1. Tana magance matsalar bacin-ciki da rashin
fitar bahaya maisa tsugunni
a bayi.
(Ayi shayin na'a-na'a ko azuba manta cikin shayi
marar madara.)
2. Tana saukake narkewar abinci
3. Maganin tuka
4. Maganin gudawa
5. Maganin mura da tari [da kuma mura mai
damun makoshi - wato 'sore throat']
(ayi amfani da man na'a-na'a ko ganyen , a tafasa
ganyen ayi shayi marar madara
, haka kuma, za'a iya amfani da man na'a-na'a
cikin ruwan zafi, ayi turiri,
a lullube da mayafi).
6. Maganin ciwon-kai ( a shafa manta wajen da
kai ke ciwo).
7. Maganin ciwon-jiki ( a shafa manta ga jijiyoyin
jiki dake ciwo
ko wajen dake damunka da ciwo, zata sanyaya,
insha Allahu).
8. Maganin ciwon-hakori (ayi amfani da man na'a-
na'a da auduga,
a diga man ga auduga , sa'annan a lika ga hakori
mai ciwon).
9. Maganin kaikayi
10. Korar sauro ( a shafa man na'a-na'a ga jiki -
hannuwa da kafafu , sauro zai gujesu)
11. Kashe tsutsar ciki
12. Taimakawa hanta wajen aiki
13. Rage yawan damuwa
- tana sanyaya rai da hana damuwa
( a tafasa ganyen
na'a-na'a ayi shayi, ko manta a zuba cikin kofin
shayi , safe da yamma).
14. Tana taimakawa kwalwa wajen rike karatu da
kaifin fahimta (ayi shayi da ganyen na'a-na'a a
rinka sha da zuma).
15. Tana sanya girki yayi kamshi - filebo ( ayi
amfani da ganyen wajen girki).
Hakan zai taimaka wajen son cin abincin
(appetite), musamman ga wanda
baya son cin abinci.
16. Tana maganin ciwon-ciki , musamman ga
mata masu matsalolin al'ada.
17. Da sauransu.
Rahamaniyya Islamic medicine Funtua.
Monday, 24 October 2016
Amfanin naa naa
Tags
About Aljeriyan Islamic chemist Kano
Sora Blogging Tips is a blogger resources site is a provider of high quality blogger template with premium looking layout and robust design. The main mission of sora blogging tips is to provide the best quality blogger templates.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment