Full-Width Version (true/false)

Breaking

Saturday, 22 October 2016

Amfanin zuma

Amfani zuma tafuskar Kara Lafiyar jiki dakuma magani, abincike na wasu likitocin muslunci. Domin rage kiba sukace sai asamo zuma mai kya kullum dasafe sai mutum yasha cokali daya na zuma, bayan yasha sai kuma yasha shayi kofi daya, kokuma Idan zai Sha shayin sai yazuba Khal tuffa cokali daya. Wanda yake so yakara samun karfin jiki akoda yaushe, yarabu da yawan kasala sai yasamo zuma yarika shan cokali daya da sassafe. Bangaran fitsarin kwance na yara Idan ana bama yaro zuma mai kya cokali daya dasafe, daya da yamma insha Allah yaro zairage yawan fitsarin dayake Idan aka dage da bashi insha Allah zai iya bari gaba daya. Wadanda kuma Allah yajarabce su da cutan kansa sai sami zuma sudinga Shanta tare da ainufin tuwanta. Dangane da ciwon hanta ko ciwon koda sai asamo zuma mai kya kullum yarika shan cokali 7 biyu dasafe 3 darana 2 da yamma. Bayan haka wanda yake da matsalar rashin narkewar abinci shima wannan hanya zaibi. Idan anaso asami waraka tafuskar matsalar kuraje naciki dawaje kamar (taipot, Ulser) sai asamo zuma arika shan gram 200,60 dasafe darana 80 ,60 dayamma Allah zai warkar dashi insha Allah. Zubar yawu hakanan, dakuma ciwon gabbai, sai asamo zuma ahada cokali 3 da man zaitun cokali 2 lemon tsami cokali biyu zaa zuba cikin ruwan dumi har wata biyu ko uku .mai fama da dayawan damuwa ko bacin rai, ko karamara hauka wannan hanya zaibi. Hakika zuma taasali maikya Allah (swt) yana cewa :يخرج من بطونها شراب مختلف ألوانه،فيه شفاء للناس.maana cewa abinda yake fita daga cikin ta wani nauin abin Sha mai launi daban daban, to wannan abun warakane zuwa ga alumma. Suratul nahal. Hakika dukkan abinda Allah s.w.t.yace warakane wajibine kowanne musulmi mai imani yayarda da wannan.Haka kuma shima dukkan abinda Manzon Allah s.a.w.yace ana samun waraka daga wannan abun dole musulmi yayi imani dashi. Hadisi yatabbata acikin (Bukhari) wani bawan Allah cikin sa yana ciwo daaka fada ma Manzon Allah s.a.w.sai yace abashi zuma, aka bashi, ciki yakara ciwo, aka fada masa yace akara masa, yakaradai, aka Kara fada masa, yace Allah yayi gaskiya, cikin dan uwanka karya yake, yace aje akara basa, ana bashi sai ciki yadaina ciwo. Wallahu aalam.

No comments: