Full-Width Version (true/false)

Breaking

Saturday, 22 August 2026

Bayani akan yanayin shafar jinnu da Hassada

Ta yaya zamu tabbatar da hakikanin samuwar cutar hasada?
Da kuma bambance abinda yake nagaskiya acikinta ba kamar yadda wasu suke musawa
ba.
Kashi na biyu babi na 9!
Wasu Suka ce: Wannan duk hasashe ne kawai, ba shi da wata hakika. Masu irin wannan
ra'ayi kuwa su ne mafi jahilcin mutane wajen ji da hankali. Wasu daga cikinsu sun fi kowa
sauƙin zuciya da kyawawan halaye, amma sun fi kowa nisa da sanin al'amuran ruhohi,
rayuka, sifofinsu da tasirinsu.
Yaya hassada take faruwa daga mai hassada?
Masu hankali daga cikin mutane, duk da bambancin addinansu da akidunsu, ba sa musun
samuwar cutar ido (ain). Ko da yake sun bambanta wajen bayyana dalilinta da yadda take
aiki.
Wasu suka ce:
Wanda yakasance yana da gubar idanu idan ya daidaita kansa a kan wani mugun yanayi,
wani irin ƙarfi mai cutarwa yana fitowa daga idanunsa ya isa ga wanda aka yi wa yayi ma
wannan kallon,da kuma ketar, sai ya cutar da shi.
Wannan ba abin mamaki ba ne; domin kamar yadda aka tabbatar cewa akwai wasu nau'ikan
macizai masu fitar da guba ta hanyar numfashi ko kallonsu har su kashe mutum, haka ma
ba abin mamaki ba ne idan kallon mai ido ya yi tasiri ga wanda ya kalla musamman ma idan
da wata manufane.
Wasu kuma suka ce:
Ba za a yi nisa da cewa daga idon wasu mutane akwai wasu siraran ƙwayoyi ko ƙarfi marar
ganuwa da ke fita, su isa ga wanda aka yi wa kallon, su shiga cikin ramukan jikinsa, daga
nan kuma su jawo masa lahani.
Sauran kuma suka ce:
Allah Madaukakin Sarki Ya sanya al'ada cewa idan mai ido ya kalli wani da idonsa, Allah
Yakan halitta wani abu mai tasiri wanda ke haddasa cutar ga wanda aka kalla, ba lallai sai
an samu wani ƙarfi da yake fita daga idon mai ido ba.
Wannan shi ne ra'ayin waÉ—anda suke tabbatar da cewa akwai dalilai da abubuwan da suke
da tasiri a cikin wannan duniya.
Suka ce:
Tasirin mai hassada ga wanda akewa hassada ba ya musantuwa sai dai wanda ya kauce wa

No comments: